/

Tarihi: Asalin Kunnuwa biyun Rawani, Tagwayen Masu da Takalmin Jimina

dakikun karantawa
Tarihin Rawani
Marigayi Ado Bayero - San Kano

Tagwayen Masu wasu masu ne guda biyu da suke a hade kuma yanzu ya zama shi ne abu mafi mahimmanci a gidan sarautar Kano wanda yake nuna duk wanda ya mallake su shi ne Sarki.

Babu wanda zai rike Tagwayen Masu kuma ya yi amfani da su sai Sarkin Kano.
Kuma kaf masarautun da ke karkashin daular Usmaniyya da ma ta Hausa ba wanda ke da hurumin amfani da su in ba gidan sarautar Kano ba.

Wana Sarkin Kano ne ya fara rike Tagwayen Masu?

Bayan mutuwar Sarki Gijimasu a shekara ta 1133 sai tagwayen ‘ya’yansa, Nawata da Gawata suka gaje shi. Tagwayen sarakuna lokaci daya akan karaga.

Launin mashin da kowanne daga cikinsu ke rikewa ya banbanta. Daya yana da launin Ja wanda yake nufin ubangijin yaki, dayan kuma yana da launin kore, wanda yake nufin ubangijin yabanya, kamar yadda wani jinin gidan sarautar Kano mai binciken tarihin masarautar, Kasim Tijjani Turaki ya bayyana.

Sarakunan sun yi mulki ne na tsawon shekara biyu. Wasu masana tarihin na cewa daya daga cikinsu ne ya fara mutuwa, sai dayan ya hade masun guda biyu yake rike wa. Sun yi mulki ne gabanin zuwan addinin musulunci.

To sai dai wasu masana tarihin na cewa sun mutu ne lokaci daya, kuma bayan mutuwarsu ne kaninsu Sarki Yusa ya gaje su a shekara ta 1135 inda ya hada wadannan masun waje daya ya rike su a matsayin tagwayen masu.

Ya mulki Kano tsawon shekara 58 kuma tun bayan rasuwarsa a shekara ta 1193 ba a sake dauko tagwayen masu ba sai lokacin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa a shekara ta 1462, a cewar Kasim.

Asalin Takalmin gashin jimina:

Sarakunan Kano sun kwaikwayo amfani da takalmin gashin jimina ne daga sarakunan Borno, wadanda su kuma suka kwaikwayo daga sarakunan daular Usmaniyya ta Turkiya, a cewar Dakta Tijjani Naniya.
Ba wanda ke sa takalmin gashin jimina sai sarkin Kano, babu kuma wanda ke rike tagwayen masu sai Sarki.

Rawani mai kunne biyu

Rawani mai kunne biyu ya samo asali ne a lokacin sarakunan Fulani. Kuma wasu bayanai na cewa rawanin yana nuna tamkar sunan Allah ne.
Kewayen rawanin yana nufin Hakuri, kunnuwan biyu kuma suna nufin lam guda biyu, ma’ana lillahi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog