(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');
//

#RanarHausa: Hukumar gasar kwallon kafa ta Laliga ta taya al’ummar Hausawa murna

Karatun minti 1

Hukumar gasar kwallon kafa ta Laliga dake kasar Andulus wato Spain ta taya daukacin al’ummar Hausawa dake fadin duniya murnar bikin Ranar Hausa da yake gudana.

Rahoton Dabo FM ya bayyana hukumar ta Laliga ta misalin karfe 3 agogon Najeriya, 26 ga Ogusta ta fitar da sakon taya murnar ta kafafen ta na sada zumunta.

Hukumar gasar Laliga ta bayyana Hausa da kyakkyawan yare, ta kuma kara da cewa “A wannan shekara ta Ranar Hausa ta Duniya, muna taya da duk wanda yake magana da kyakkyawan yare! 🎉”

Wannan sako dai ba karamin farantawa Hausawa rai zai yi ba, musamman masu kallon gasar kwallon kafa a fadin Duniya baki daya.

An ware kowacce ranar 26 ga Ogusta matsayin Ranar Hausa ta Duniya, duk da dai Majalisar Dinkin Duniya bata bada lasisi ba, amma mutane da yawa na ganin wannan dama ce da zata kara daga Harshen Hausa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog