Da dumi-dumi: Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalissar tarayyar ya koma APC daga PDP

Karatun minti 1
Yakubu Dogara

Tsohon kakakin majlissar tarayyar Najeriya, Rt Hon Yakubu Dogara ya bar jami’iyyar PDP zuwa jami’iyyar mai mulki ta APC.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan da suka gana da shugaba Muhammadu Buhari da shugaban riko na jami’iyyar APC, Mai Mala Buni – gwamnan jihar Yobe a fadar gwamnatin dake tarayyar Abuja.

Alhaji Mai Mala Buni ne ya shaidawa manema labarai ficewar tsohon kakakin majalissar yayin da yake zantawa da manema labarai bayan fitowarsu daga ganawa da shugaba Buhari.

Gwamnan ya ce; “Yanzu Dogara ‘dan jami’iyyar APC ne.”

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog