Taskar Malamai: Mahaddata Alƙur’ani daga Sahabbai – Sheikh Hamza Kabawa

dakikun karantawa

Taskar Malamai: Mahaddata Alƙur’ani daga Sahabbai – Tare da babban limamin masallacin Juma’a na Bello Road, Sheikh Hamza Uba Kabawa.

Sanin kowa ne cewa Sahabbai su ne alarammomi na farko da suka haddace Alƙur’ani, suka kiyaye shi, suka rubuce shi, suka koyar da shi, suka yi aiki da shi sannan suka yada shi a duniya.

Akwai Sahabbai masu tarin yawa da suka haddace Alƙur’ani wadanda babu wanda ya san adadinsu sai Allah.

Wasu sun haddace shi tun Manzon Allah SAW yana raye, wasu kuwa sun kammala haddarsu ne bayan rasuwar Manzon Allah.

Hafiz Ibn Hajar, Allah ya jikansa yana cewa :-

“Babban Alaramman nan Abu Ubaid ya lissafa wadanda suka haddace Alƙur’ani daga cikin Sahabbai.

Daga cikin wadanda ya lissa cikin masu Hijira akwai halifofi guda hudu: Abubakar, Umar , Usman da Ali, sai Dalhatu, Sa’ad, Ibn Mas’ud, Huzaifa, Salim, Abu Hurairata, Abdullahi bn Sa’ib, Abadila wato Ibn AbbasAbbas, Ibn Umar, Ibn Zubair da Ibn Amru bn As.

Daga cikin mata akwai Nana Aisha, Hafsa da Ummu Salma .

Sai dai cikinsu akwai wadanda suka haddace Alƙur’ani tun manzon Allah yana raye, wasu kuwa sun kammala haddarsu ne bayan rasuwarsa.

Ibn Abi Daud ya lissafa wasu a cikin littafinsa, Al Shari’a da suka hada da Tamim bn Aws cikin masu Hijira da Uk’batu bn Amir. Cikin mutan Madina kuwa ya lissafa Ubadata bn Samit, Mu’az wanda akewa alkunya da Abu Halima, Mujammi’i bn Harithata, Fudhalata bn Ubaid, Maslamata bn Makh”lad da wasunsu.

Ya bayyana cewa wasunsu sun haddace tun manzon Allah yana da rai. Daga cikin mahaddatan akwai Abu Musa Al Ash’ariy Abu Umar Al-Adda’niy ya ambaci hakan.

Ya kuma lissafo wasu daga masu Hijira da suka hada da Amru bnl As, Sa’ad bn Abbas da Ummu Warakata ……” Fathul Bari 9/52

Za a iya duba Al It”kan na Imam Al Suyudi 1/248-249.

Ina Alarammomi da masoya alarammomi ga iyayenmu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog