/

Karatun minti 1

Wani matashi mai suna Musa Umar ya jaddada aniyar sa ta gudanar da tattaki daga karamar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna zuwa Jihar Zamfara domin saduwa da babban masoyin sa gwamnan Jihar ta Zamfara Alhaji Bello Muhammed Matawallen Maradun.

A zantawar sa da dabo FM, matashin ya bayyana cewa zuwa yanzu tafiya ta yi nisa kuma yana ganin haske a tafiyar kasancewar ya sanya kishi ne na babban masoyin nashi a tafiyar.

Ya kara da cewa, tun shekaru da dama da suka gabata yake da soyayyar Matawalle a cikin ran shi, kuma irin gagarumar nasarar da ya samu a jagorancin Jihar Zamfara ta kara karfafa masa gwiwan ganin ya sadu da shi.

Musa Umar ya sake jaddada cewa ba zai baro Jihar Zamfara ba sai ya sadu da Gwamna Bello Muhammed Matawalle duk da bai san kowwa ba a Zamfara.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog