Kungiyar Kano Pillars ta ‘kunyata Kanawa’ a wajen kaddamar da Rigar wasannin kakar 2020-2021

dakikun karantawa

A jiya Alhamis, Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta fitar da sabbin rigunan da kungiyar za ta taka leda da su a kakar wasannin shekarar 2020-21.

DABO FM ta tattara cewa shugaban Kungiyar, Alhaji Surajo Shu’aibu Jambul ya kaddamar da sabbin rigunan yayin taron shugabancin gudanar tare da masu ruwa da tsaki na kungiyar a ofishinsa dake Sakatariyar Kungiyar a birnin Kano.

Kungiyar ta ce ta cimma yarjejeniya da wani kamfani na kasar Turkiyya wanda za rika yi wa kungiyar kayyakin wasanninsu.

Sai dai yadda aka kaddamar da rigunan  bai yi wa magoya bayan kungiyar dadi ba har ma suka kirashi abin kunya duba da yanayin da aka bi babu tsari a ciki kamar yadda za ku gani a hotuna.

Da kungiyar take sanarwar a shafinta na Instagram, wadanda suka yi martani sun yi kira da Kano Pillars da ta sauya hotuna da kungiyar kamar a Najeriya ta kasa daukar mai hoton kirki da zai dauki kaddamar da kayyakin wasanni.

Wasu daga masu martani a shafin kungiyar, Ademola Pelumi Ibrahim ya ce; “Mai gudanar da shafin nan kana ba wa harkokin wasanninmu kunya, ka duba Allah ka goge wannan shirmen.”

Yahaya Usman kuwa cewa yayi: Gaskiya ba mu da kayan aiki, ba mu da Kyamara masu kyau.”

A wani labarin kuma za ku ji cewa gwamntin jihar Bauchi ta amincewa Kano Pillars yin amfani da filin wasa  Abubakar Tafawa Balewa domin kungiyar Kano ta buga gasar Confederattion Cup na kakar 2020-21.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog