Tsugunno: Masu nadin Sarki a masarautar Kano sun maka Ganduje a kotu

Hudu daga cikin manya masu nadin Sarki a masarautar Kano sun mika gwamnan jihar, Dr Ganduje, zuwa kuliya manta sabo akan karin masarautu 4 da yayi a kwanakin da suka gabata.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa masu nadin sarkin wadanda suka hadar da Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan, Madakin Kano, Yusuf Nabahani, Sarkin Dawaki mai tuta, Bello Abubakar da Makaman Kano, Sarki Abdullahi.

Sun bayyana cewa karin masarautu guda 4 da Gandujen yayi, wani mataki ne na ruguza tarihin jihar Kano musamman cire daraja da rage mukaman sauran basarakai dake masarautar.

Masa karar sunce sun barranta da matakin karin masarautun da gwamnatin tayi kuma sun daukin matakin bisa wakilcinsu na gidan Sullubawa, Yolawa da Dambazawa.

Masu Alaƙa  A matsayi na, na 'dan Dagaci, tayaya mutane zasu ce zan rushe ko ruguza Masarauta? - Ganduje

Tin dai a ranar 8 ga watan Mayu ne gwamna Ganduje ya rattaba hannu a bisa dokar da majalissar jihar tayi a cikin kwana 2.

Sai dai Gandujen ya ketare wani hukuncin wata babbar kotun tarayyar dake da zama a Ungoggo wacce ta bukacin gwamnatin ta dakatar da nadin tare da kin basu takardun kama aiki a hukumance.

Al’umma dayawa suna fassara karin masarautun bisa kudirin da gwamnan yake dashi na rage darajar Sarki Muhammadu Sunusi II.

Hakan na zuwa ne bayan da tsagin gwamnatin suka zargeshi da goyon bayan jami’iyyar PDP a zaben gwamnan da aka gudanar a jihar.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Masu Alaƙa  Hukumar yaki da Cin hanci ta jihar Kano ta bukaci a dakatar da Sarki Sunusi

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: