(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Wani mutum ya kone kanshi saboda tsananin talauci a jihar Ebonyi

Karatun minti 1

‘Yan sanda a jihar Ebonyi suna gudanar da bincike kan rahoto da suka samu na wani mutum daya kone kanshi a jihar saboda baya iya ciyar da kanshi.

‘Yan sanda sunce sun samu labarin Chinedu Nweze wanda ya kone kanshi bisa tsananin talauci daya kaishi ga cinnawa kanshi wuta a kusa da ajin wata makarantar Firamare a garin Abakaliki.

Sai dai ‘yanda sunce suna gudanar da bincike don gano ainahin dalilin daya saka mutumin kona kan nashi.

Jaridar Sahara Reporters ta tabbatar da cewa tabbas Mr Chinedu ya kone kanshi bisa talauci bisa magana da sukayi da saidun gani da ido.

Makotan Mr Chinedu sunce tin kwanakin baya yake musu korafi kan cewa baya iya ciyar da kanshi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog