//
Wednesday, April 1

Lemon Tsami yana kare jiki daga daukar cutar “Cancer”, Daga Dr Guru Prasad

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Dr Guruprasad Reddy, babban Likita na bangaren zuciya da sanin kwayar halittar dan adam a makarantar lafiya ta OSH dake kasar Rasha, ya kammala binciken dake gudanar akan ciwon Daji wato Cancer.

Dr Prasad yace,”Nayi iya yi na wajen kammala wannan binciken, ina fatan za’a taimaka wajen aiwatar dashi domin gudun fadawa hadari.

Ga daga cikin jerin shawarwari da abubuwan da za’ayi ko za’a daina kamar yadda likitan ya fitar.

“Shan ruwan leman tsami mai zafi yana kare jiki daga ciwon daji. Shan leman tsamin da zafi yafi sha a sanyi.

 1. Cin abinci da daddare sosai yana kara bada damar kamuwa da dajin ciki.
 2. Kada a rika cin kwai ya wuce guda 4 a mako.
 3. Kada a ci kayan marmari bayan an kammala cin abinci. Ana cin kayan marmari ne kafin aci abinci.
 4. Mata su guji shan shayi a lokacin da suke al’ada.
 5. A guji cin Tumatur lokacin da ake jin yunwa.
 • A lazimci shan kofin ruwa duk safiya kafin a ci komai.
 • A bada ratar awa 3, tsakanin cin abinci da kwanciya bacci.
 • Shan giya kadan ko kaurece mata saboda bata wani nau’in amfani a jiki, sai dai takan kawo hawan jini da ciwon siga.
 • Kada a rika cin gashashen Biredin da aka gasa a injin Oven.
 • Kada a kwanta a kusa da wata na’ura da akeyiwa charji kamar Wayar salula da sauransu.
 • A lazimci shan ruwa a kowacce rana, ayi kokarin shan kofi goma ko sama a rana.
 • Kada a yawaita shan ruwa da daddare. An fiso a sha ruwa dayawa da rana.
 • Kada a rika shan Coffee sama da sau biyu a rana. Ya hana isasshen bacci tare da ciwon ciki mai kama da na ulcer.
 • Kada a durfafarwa cin abinci mai maiko. Abinci mai maiko yana daukar jiki sama da awa 5 kafin ya nike shi.
 • A rage ciye ciyen abinci da zarar karfe 5 na yamma ya gota.
 • A yawaita cin Inibi, Kabewa, Allayahu, “Peach, da Ayaba. Mai ciwon siga kada ya tsanantawa Ayaba sosai.
 • A yi kokari wajen yin baccin sama da awanni 8 a rana.
Masu Alaƙa  Yadda za mu kare kan mu daga kamuwa da cutar zazzabin 'Lassa' -Dr Abdul'aziz T. Bako

Ruwan Lemon Tsami mai zafi yana kashe kwaiyar sinadarin Cancer

Ruwan Lemon Tsami mai zafi yana kara lafiya da karfin jiki da saka tsawon rai.

Ruwan Lemon tsami mai zafi yana hana girman ciwo da tabo.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020