Wani tsageran ɓera mai halayyar cin ganyen wiwi ya tsinci kansa a gidan gyaran hali

Karatun minti 1

Colin Sullivan, manomin tabar wiwi a kasar Canada ya damke wani tsageran bera da yayi kaurin suna wajen lallabawa ya satar masa ganyen tabar wiwi a gonarsa.

Rahoton Dabo FM ya bayyana wannan manomi ya share tsahon sati 2 yana fakon barawon dake masa satar wiwi inda ya gano wannan tsageran bera ne bayan ya kamashi yaci ya yi mankas.

Mr Colin ya bayyana daga nan ne ya dauki wannan bera zuwa gidan gyaran hali, a inda ya share kwanaki shida a kulle, bayan ya tsallake wasu tsare tsare 12 a gidan gyaran halin, daga bisani aka sake shi.

Da yake karin bayani, Mr Colin Sullivan yace “Bayan tsahon kwanaki na yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi, wannan bera ya samu nasarar komawa cin abincin sa na gargajiya.” Kamar yadda LegitNg ta fitar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog