Buhari ya kafa kwamitin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga talauci

Karatun minti 1
Muhammadu Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamitin ajandar da Najeriya zata wanzu a kanta zuwa shekarar 2050 wanda cikinsa akwai shirin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 dagaalauci.

Rahoton Dabo FM ya bayyana wannan yazo ne bayar karewar tsohuwar ajandar da Najeriya ke kai ta 20:2020, shugaban ya nada Atedo Peterside da ministar kudi, Zainab Ahmed wadanda zasu yi jagorancin wannan tsari.

An gudanar da taron kafa kwamitin ne ranar Laraba a garin Abuja, da yake karin bayani, Buhari ya bayyana Agendar 2050 ta gaji tsohuwar Ajandar Farfado Da Tattalin Arziki Tare Bunkasa Shi ta shekerar 2017-2020.

“Aikin wannan shiri shine fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga talauci nan da shekaru 10 masu zuwa, anyi shirin ne bisa duba da hasashen Bankin Duniya na Najeriya zata zamo kasa ta 3 wadda tafi kowacce kasa yawan al’umma.”

Hasashen Bankin Duniya ya kuma bayyana nan zuwa shekarar 2050 mutanen Najeriya zasu kai milyan 400, kamar yadda shugaban kasa ya bayyana.

Daga karshe shugaba Buhari ya yi kira da shugabannin kwamitin dasu zage damtse domin fito da kimar Najeriya a Afirka da ma Duniya baki daya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog