Yadda aka kama wasu guggun yara ɓarayi ‘yan kasa da shekara 14 a Kano

Karatun minti 1

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, ta sanar da kama wasu yara ɓarayi waɗanda shekarunsu basu wuce 14 a duniya ba ba.

DABO FM ta tattara cewar rundunar ta kama a ƙalla yara 7 da ake zarginsu da sace-sacen mutane a karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano.

Kakakin rundunar a jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya zanta da yaran wadanda duk suka amsa laifuffukansu tare da bayyana yadda su ke fasa shagunan jama’a domin yi musu sata.

Daya daga cikin jagoran ɓarayin mai suna, Halifa Iliyasu, dan shekara 14, ya ce sun bi shagunan mutane a Filin Mushe da ke karamar hukumar Gwale, su ka sato kekuna 5 da shaddoji.

Dukkanin yaran sun amsa suna shaye-shayen kayan mayen da suka hada da tabar wiwi, taba sigari da kuma madarar sikudayin.

Kiyawa ya ce rundunar tana cigaba da bincike, kuma da zarar ta kammala, za ta aike su zuwa kotu domin fuskantar hukunci.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog