Labarai

Gwamnatin Kano ta janye dokar hana cakudar maza da mata a baburan ‘Adaidaita Sahu’

Rahotonni daga fadar gwamnatin jihar Kano na cewa tuni gwamnati ta janye dokar nan ta hana cakuda maza da mata a baburan adai-daita sahu.

Rahoton mu na Dabo FM daga wata majiya mai tushe daga fadar gwamnatin jihar Kano ta shaidawa mana cewa anyi wani kwarya-kwaryar zama na musamman a yau Litinin tsakanin masu ruwa da tsaki a al’amuran addini a jihar Kano kan fara aiwatar da wannan doka.

Inda zaman ya cimma matsayar janye dokar har zuwa wani lokaci -Kamar yadda Freedom Radio ta tabbatar.

Kafar ta nemi jin ta bakin babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina wanda ya ce ayi masa uzri idan Allah ya kaimu gobe Talata zasu gudanar da taron manema labarai kan dokar.

Idan zaku iya tunawa dai hukumar Hisbah ta ce zata jaddada dokar hana cakuda maza da mata a baburan adai-daita sahu daga farkon shekara ta 2020 mai kamawa.

Sai dai batun ya haifar da cece kuce, musamman a kafafan sada zumunta.

Masu Alaka

Ganduje zai tura kwararru 40 kasar Burtaniya don koyo sana’o’in da zasu koyawa Matasan jihar Kano

Dabo Online

Manyan bukatu 5 da Ganduje yake so majalisa ta zartar masa kan masarautar Kano

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu an mayar da sarakuna a Kano basu da wata daraja -Aminu Daurawa

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje na shirin ayyana Sarkin Bichi a matsayin babban sarki a Kano

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu-Yanzu: Jiga-jigen APC sun dira a Habuja da duku-duku kan shari’ar zaben Kano

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu-Yanzu: An faɗi gabana ana rokon tilas saina tumɓuke rawanin Sarki Sanusi -Ganduje

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2