Labarai

Watanni biyar da daukewar tauye hakki da akayi wa matashi Abubakar Idris ‘Dadiyata’

A wannan makon da muke ciki na shiga sabuwar shekarar 2020, Abubakar Idris Dadiyata zai cika watanni 5 tin bayan daukeshi da wadanda ba’asan ko suwaye ba sukayi.

Zuwa yanzu, dangin matashin sun kai karar Gwamnatin jihar Kaduna, hukumar DSS reshen jihar Kaduna zuwa gaban kotu domin kin bahasi biyo bayan zarge-zarge da akeyi musu na alhakin daukeshi.

Tin a ranar 3 ga watan Agustar 2019, wasu mutane da ba’a san ko suwaye ba, sukaje har gidan matashi dake jihar Kaduna suka daukeshi, lamarin da yayi sanadiyyar har zuwa yanzu babu labarinshi.

Hukumar DSS da aka zarga tin farkon dauke matashi, ta bayyana cewa bata tsare da matashin, hasalima bata tura jami’anta unguwar su Abu Dadiyata aiki a wannan dare ba.

Dadiyata, malami ne a jami’ar Katsina, ya kasance dan gwagwarmaya da fafutukar ganin gwamnatin APC a Najeriya da jihar Kano su yiwa mutanen da suke jagoranta adalci.

Abubakar Idris, wanda akafi sani da Abu Hanifa Dadiyata, dan Jami’iyyar PDP, mai bin tsari da darikar Kwankwasiyya, tsagin da akeyin ‘Kare-Jini, Biri-Jini’ irin na siyasa tsakaninsu da bangaren gwamnatin jihar Kano na Gandujiyya.

Manyan mutane a Najeriya sunyi Allah-Wadai da kamun matashin, hukumomin kare hakkin dan Adam na duniya sun biye musu sahu wajen kiran wadanda suke tsare da shi su sake shi.

Jagora a jami’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima, ya zargi wani gwamnan Arewa wanda bai fadi sunanshi ba a matsayin wanda yake da hannu wajen tsare maatashin.

Masu Alaka

Gidauniyar wasu ‘yan mata a Kano ta kai tallafin kayan abinci da tufafi zuwa gidan marayu da gidan yari

Dabo Online

Zuwa ga Shugaba Buhari: Shekaru 4 Kenan, Chanjin da muke jira yaki zuwa, Daga Nasiru Salisu Zango

Dabo Online

Borno ta doke Kano a zabe na 2 a gasar Kwalliyar Al’adu bayan ayyana zaben farko ‘Inconclusive’

Dangalan Muhammad Aliyu

‘Dan Najeriya ya kammala karatu da sakamako mafi kyau a Jami’ar kasar Indiya

Dabo Online

Zane-zane na basira da ‘dan Arewa Abbas Nabayi mai shekaru 21 yake yi

Dabo Online

Rigar ‘Yanci: Abba Gida Gida ko Executive Mai Sinƙe?, Daga A.M. Fagge

Dabo Online
UA-131299779-2