0
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya janye aikin daya bawa Mr Festis Adebayo cikin kasa da awanni 48 bayan ya bashi mukamin mai bashi shawara a fannin labarai.
A wata sanarwar da ofishin shugaban majalissar dattawan ya fitar a ranar Alhamis mai dauke da sa hannun Muhammad Isa, sanarwar tace Sanata Ahmad Lawan ya janye mukamin daya bawa Mr Festis kamar yadda Daily Post ta bayyana.
