Siyasa

Mun barwa Allah komai shiyasa hankalinmu yake kwance kan batun Shari’ata – Abba Gida Gida

Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jami’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf yace hankalishi a kwance yake akan batun shari’ar da take gaban kotu da yake kalubalantar zabe da Dr Ganduje ya lashe.

Abba ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da sashin Hausa na BBC akan batun korar kara da ake kalubalantar takararshi a PDP ta jihar Kano.

Hukuncin kotun kolin dai ya tabbatar dashi a matsayin halastaccen dan takarar jami’iyyar a jihar Kano.