Siyasa

Aisha Buhari ce ta assasa cire mukamin da Sanata Ahmad Lawan ya bayar

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya janye aikin daya bawa Mr Festis Adebayo cikin kasa da awanni 48 bayan ya bashi mukamin mai bashi shawara a fannin labarai.

Tin bayan nadin ne dai ‘yayan jami’iyyar APC sukayi da cece kuce bisa cewa Mr Adebayo baya tafiyar shugaba Buhari.

Sai dai DABO FM ta binciko cewa mai dakin shugaba Muhammadu Buhari, Haj Aisha Buhari, tana daga cikin wadanda suka assasa har Sanata Ahmad Lawan ya janye mukamin daya bawa Mr Adebayo.

Binciken ya gano cewa Haj Aisha Buhari ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Twitter inda ta goyi bayan wadansu matasan APC da suka gudanar da zanga-zanga akan sukar mukamin da Sanata Ahmad Lawan ya bayar.

“Baza ka iya tafiyar da tsarinka tare da mutanen da basa goyon wannan tsarin naka ba. Tayaya zaka cimma abinda kake so tare idan har ka kusanta zuwa ga wadanda sukayi yakin rugujewar tsarin naka.

Karin Labarai

Masu Alaka

Aisha Buhari ta halarci taro da rigar naira miliyan 1.6

Dabo Online

Iyalan Buhari na da damar daukar jirgin shugaban kasa suyi harkokin gaban su -Garba Shehu

Muhammad Isma’il Makama

Aisha Buhari ta yiwa Mamman Daura da Garba Shehu kaca-kaca a Villa

Muhammad Isma’il Makama

Aisha Buhari zata gina katafariyar Jami’ar Kudi mai zaman kanta

Dabo Online

Hanan Buhari ta kammala digiri da maki mafi daraja

Muhammad Isma’il Makama

Hannunka Mai Sanda: Aisha Buhari ta kara caccakar shugaba Buhari

Dabo Online
UA-131299779-2