Home BincikeMansura Abdulaziz, ta Jami’ar Bayero a Kano ta gano maganin cutar ‘Cancer’ daga Itatuwan Gargajiya

Mansura Abdulaziz, ta Jami’ar Bayero a Kano ta gano maganin cutar ‘Cancer’ daga Itatuwan Gargajiya

by Dabo Online
0 comments

Mansurah Abdulaziz, kwararriya kuma masaniyar kwayoyin halitta dake aiki a cibiyar bincike sashin ‘Biotechnology’ na Jami’ar Bayero dake Kano, ta yi gagarumin kokari waje taimakon kawar da cutar ‘Cancer’.

Kwararriyar masaniyar kwayoyin halittar tayiwa Jaridar The Guardian bayani dalla-dalla kan binciken ta na samar da maganin ‘Cancer’

Mansurah Isah, itace wacce ta lashe gasar bincike ta Najeriya tare da lashe tsabar kudi na dalar Amurka 86,000 a watan Yuni, jim kadan bayan amsa gayyatar aikin karawa juna sani da tayi a kasar Andalus a Nuwambar 2018.

Da take bayani akan tushen Iliminta na bangaren kimiyya, Malamar ta shaida cewa tin a lokacin da take tasowa take son bangaren kimiyya, inda ta shaida cewa ta taso da niyyar zama cikakkiyar Likita, amma daga karshe tayi karatun ‘Biochemistry’ a Jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria na jihar Kaduna.

DABO FM ta tattaro cewa; Mansurah Abdulaziz ta bayyana cewa tin da fari, binciken nata ya bada karfi ne wajen gano sinadaren da zasu yaki cutar ta ‘Cancer’ daga dangogin tsirai kamarsu Zogale da Fasadabur.

Ta kara da cewa binciken nata yayi duba game irin aiki da bishiyoyin zasu yi waje yakar ‘Cancer’ a jikin dan Adam, inda ta kara da cewa babu wata Illa ko wahalar da bishiyoyin zasuyi yayin amfani dasu.

Da take amsa tambayar, Ko meyasa tafi karkata wajen bincikenta da Bishiyoyi da Tsirai na Nahiyar Afirika? Malama Mansura ta amsa da cewa “Suna dauke da sinadarai dayawa wadanda har yanzu ba’a fara karatunsu ba.

“An yi bincike cewa wadannan ‘ya ‘yan itatuwan suna da manya-manyan sinadaren yakar cutar Cancer. Binciken magungunan gargajiya kamar Sabara, wacce masu magani a nahiyar Afirika suke amfani da ita, an fitar da magungunan ‘Cancer’ dayawa daga wannan itacuwar.”

“Ina gani hakan ya nuna cewa karantar bishiyoyin Afirika zai kawo cigaba wajen samar da magunguna dayawa.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00