Man Utd ta baiwa Inter Milan aron Alexis Sanchez

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Alexis Sanchez ya kammala tafiya kungiyar Inter Milan ta kasar Italiya da taka leda.

Kungiyar Man Utd ce ta sanar da tafiyar dan wasa a shafukanta na sada zumunta a ranar Alhamis, 29 ga watan Agustar 2019.

<\center>

Sai dai tin kafin kungiyar ta bayar da sanarwar tafiyar dan wasa, ya riga da ya wallafa sakon bankwana ga magoya bayan kungiyar ta Manchester United.

Masu Alaƙa  Barcelona zata kece raini da Manchester United

Tin dai bayan zuwan dan wasan a lokacin tsohon mai horas da kungiyar, Jośe Mourinho, tauraruwar dan wasan ta daina haskawa duk kuwa da makudan kudaden dayake karba daga kungiyar.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.