Virgil van Dijk ya doke Messi da Ronaldo wajen lashe kambun gwarzon shekara

Dan wasa mai tsaron baya na kasar Holland, Virgil van Dijk ya lashe kambun na gwarzon shekara a tarayyar Turai.

Dan wasa Cristiano Ronaldo da Lionel Messi ne suke a matakin na biyu da na uku.

Hukumar kwallon kafa ta Tarayyar Turai “UEFA” ta sanar da Virgil van Dijk a matsayin wanda ya zama gwarzon dan wasanta na kakar shekarar 2019/2019 a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta 2019.

A taron da aka gudanar a dakin taro na Grimaldi Forum dake birnin Monaco na kasar Faransa, UEFA ta sake bayyana Virgil van Dijk , a matsayin dan wasa mai tsaron bayan da yafi kowanne.

Zuwan Virgil van Dijk kungiyar Liverpool ya sanya shi zama dan wasan baya daya fi kowanne dan wasa tsada a duniya, yayin da ya taimkawa kungiyar ta lashe kofin Zakarun Nahiyar Turai da ta dade tana muradin lashewa.

Hakazalika, dan wasan ya taimakawa kasarshi ta Holland kai wa ga mataki na karshe a gasar kofin kasashe na nahiyar Turai, wanda kasar Portugal ta doke ta a wasan.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.