0
Tsohon shugaban kasar Zimbabuwe shugaba Robert Mugabe ya Rasu.
Robert Mugabe mai Shekaru 95 a Duniya, shi ne shugaban da yayi fice wajen kawo wa al’ummar kasar ‘yancin kan su.
Ya rasu bayan fama da jinya kamar yadda iyalansa suka fitar da sanarwar.
An dai kifar da Gwamnatin Mugabe a watan Nuwambar shekara ta 2017, wanda ya kawo karshen Mulkinsa da yai zango 3.
An haifi Shugaba Mugabe a ranar 12 ga watan Fabarairu na shekarar 1924.
Yayi zaman Gidan kasu, ba tare da an yanke masa hukunci ba, saboda laifin sukar Gwamnatin kasar a 1964.
A shekarar 1973, a lokacin yana Gidan Yari aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar ZANU, wanda yana daya daga cikin iyayen Jam’iyyar.
