‘Yan Bindiga sun harbe mutum tare da garkuwa da mutane 12 a titin Abuja-Lokoja

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun tare hanyar Lokaja zuwa Abuja tare da kashe mutum da sace wasu mutanen.

Lamarin ya faru ne a daidai Kauyen Omoko dake da nisan Kilomita 4 in kabar Abaji, a yankin babban birnin tarayya Abuja.

Sun dai tare mota Kkwamfiyuta ne mai cin mutane 18 a ranar Lahadi da misalin karfe 4 na yamma.

Wani da ya tsira a cikin motar mai suna Adesoji Rufus, ya tabbatarwa Jaridar Daily trust cewa, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi bayan suna kan hanyar su ta zuwa Abuja daga Ikko.

Ya ce yana cikin tuka motarsa Toyota a wannan hanyar, sai ya ji maharan sun fito ta cikin daji dauke da manyan makamai suna ta harbe-harbe.

Masu Alaƙa  A tantance jami'an tsaro domin ana zargin akwai hannun su a hare hare -Sheikh Sani Jingir

Ya ce, a kalla maharan sun rufe hanya ya kai na tsawon mintuna 30, babu wani jami’in tsaro daya tunkaro wurin.

Wani da ya ga abin a idonsa, yace maharan sun harbe mutum guda, tare da diban mutane 12 zuwa cikin daji.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kogi, Williams Aya, ya tabbatar aukuwar lamarin, in da yace, ‘yan fashi ne, kuma suna nan suna kan bincike.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.