Labarai

Sama da rabin Kudaden Najeriya suna zuwa ne daga Hukumar Tara Haraji ta Kasa

Hukumar tara haraji ta kasa wato FIRS, ta ayyana cewa sama da rabi kudaden da Najeriya ke samu suna zuwa ne daga wurinta.

Shugaban wayar da kan jama’a da kuma rarraba kudade na hukumar Mr. Elias Mbam ne ya tabbatar da haka. Inda yace hukumar su tana Samar da kaso 59.7 na kudaden da Najeriya take rarrabawa a watanni uku da suka gabata.

Mr Mbakam ya bayyana haka ne a babban birnin tarayyar Abuja, lokacin da ya ziyarci Mr. Babatunde Fowler shugaban hukumar tattara haraji ta kasa a ofishinsa.

“A watanni uku da suka gabata, mune hukumar da tafi kowacce hukuma ba da gudunmawar kudaden da Najeriya ke amfani da su, da kaso 59.7 cikin 100.”

Karin Labarai

UA-131299779-2