Home LabaraiBudurwar Zamfara da ta kona kanta tana samun kayatattun kyaututtuka da tallafin Kudade

Budurwar Zamfara da ta kona kanta tana samun kayatattun kyaututtuka da tallafin Kudade

by Dabo Online
0 comments

Manyan mutane masu fada aji, sun shiga samun masu taimakawa dangin budurwar nan data kona kanta a jihar Zamfara.

Mahaifin budurwar, Aminu Muhammad, ya bayyana tallafin kudin a matsayin wanda zai rage musu wahalhalun biyan kudin samun lafiyar ‘yar tashi. – Caliphate Trust ta tabbatar.

A ranar 8 ga watan Satumbar 2019 ne sai Budurwar ta cinnawa kanta wuta bayan da saurayinta ya shaidawa mahaifinta cewar bashi da kudin da zai iya aurenta.

Tin dai lokacin da al’a ya faru, mahaifin budurwar ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar; Bashi da kudin da zai iya daukar dawainiyar lafiyar diyartashi.

Tin da fari dai mahaifin Aisha yace bayan sun gwada maganin gargajiya ba’a dace ba, sun kaita babban asibitin Gusau, inda take karbar kulawa a yanzu.

“Mun samu tallafi daga wasu mutane da basu san ko suwaye ba daga jihohin Jigawa, Abuja da garin Gusau.”

“Tallafin kudi daga tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Ibrahim Wakalla Muhammad, Sanata daga makwabciyar jiharmu ta Sokoto.”

“Mun gode kuma duk mun yaba musu duka.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00