Labarai

‘Yan arewa 123 da aka tsare a Legas sun ce basa son karar da aka shigar a madadinsu

‘Yan Arewa 123, da gwamnatin jihar Legas ta tsare yayin da suke shiga jihar, sun bayyana cewa; basa son karar da Lauyoyi kwato musu hakki suka shigar a madadinsu.

A makon farko na watan Satumba, wasu Lauyoyi ‘yan kishin kasa, ciki har da matashin nan Abba Hikima, suka mika gwamnatin jihar Legas akan batun tauye hakkin ‘yan Arewar su 123 da gwamnatin ta tsare ba bisa ka’ida ba.

DABO FM ta tattaro cewa; Gwamnatin ta saki mutanen su 123 bisa rashin kama su da laifi ko kayan laifin, sai dai ta cigaba da rike babura 48 da aka kama mutanen dare dasu.

Gwamnatin jihar dai ta cigaba da rike baburan a matsayin garkuwa da kuma sharadin janye karar da suka kai gwamantin jihar.

“Tin da fari, gwamnatin jihar Legas ta bayar da sharadin, bazata saki Baburan ba har sai mun janye karar da muka shigar. Sharadin da muka ki yarda dashi.” – Barista Abba Hikima

“Daga baya gwamnatin ta zugasu(Yan Arewa 123) suka bijirewa mana tare da alkauranta sakin baburan nasu idan har Lauyoyinsu suka janye karar da suka maka gwamnatin jihar a Kotu.”

“Ni da kai na nayi kokari fahimtar da ‘yan Arewa akan idan aka bi abin a sannu, dole baburansu zasu dawo garesu tare da biyansu diyya, amma basu gane abinda nakeson nuna musu ba.”

“Sun fi gane Kwai a baka yafi kwai a akurki.”

Barista ya kara da cewa, wasu daga cikin ‘Yan Arewa 123 da aka tsare, sun kirashi, tare da yi masa magana irin ta bijirewa da bore akan kin amincewa da bukatar gwamnati na janye karar.”

Sun bayyana masa cewa; “In dai dan mu akeyi, to mun yafe, a janye karar kawai su bamu baburanmu.”

Tini dai Barista ya bayyana sun janye karar, inda ya bayyana itama gwamnatin jihar Legas ta cika alkawarinta na sakin baburan mutanen tare da basu hakuri wanda duniya zata shaida.

Idan ba’a manta ba;

Barista Abba Hikima ya shigar da karar a madadin mutanen 123, inda ya nemi kotu ta bayyana tsare mutanen ba tare da sun yi wani laifi ba a matsayin cin zarafinsu da kuma take ‘yancinsu na yin bulaguro zuwa kowanne sashen kasa domin zama ko yin halastacciyar sana’a, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya basu iko.

Ya kuma bukaci kotu ta bukaci tilastawa gwamnatin jihar Legas bawa ‘yan Arewa 123 da ta tsare hakuri tare da biyansu diyyar Naira biliyan daya da kuma hana gwamnatin jihar da jami’inta kara tsare wani daga cikin mutanen ko kuma tsangwamarsu ta kowacce irin hanya.

Comment here