Labarai

An koka game da yadda Dan Sanda ya Bindige Dan Achaba har Lahira

Majalissar Dokoki ta Bihar Jigawa ta koka game da yadda wani Dan Sanda ya harbe wani Dan Achaba har Lahira a makon da ya gabata.

Lamarin dai ya faru a birnin Dutse ne na jihar.

Banayan Harbin Dan Achabar dai ‘yan uwansa sun gudanar da zanga-zanga da ta tilastawa ‘yan Sanda arcewa ba shiri.

Dan majalissar jiha mai wakiltar karamar Hukumar Dutse Hon Musa Sule Dutse ne ya gabatar da koken, in da yayi kira ga majalissar da ta bibiyi lamarin domin ayi. Wa Dan Achabar adalci.

Jaridar Dabo FM tayi ta kokarin jin ta bakin kakakin Hukumar ‘yan Sanda ta jihar Jigawa, SP Abdul Jinjiri amma hakan bata samu ba.

‘Yan majalissar sun nuna rashin jin dadin su, na wannan abun, sannan sun yi kira ga Hukumar ‘yan Sanda a kan ta gudanar da bincike na Gaskiya a kan lamarin

Comment here