Tsohon mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar Najeriya a tutar jami’iyya PDP, Buba Galadima, ya bayyana dalilinshi na zaben Sanata Rabi’u Kwankwaso a zaben fidda gwanin APC na shekarar 2015.
Buba Galadima, babban jigo a yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari na shekarar 2015, ya bayyana cewa ya zabi Kwankwaso bisa dalilin cewa yafi shugaba Muhammadu Buhari chanchanta jagorantar Najeriya.
“Nayi wa Kwankwaso aiki a zaben fidda gwanin jami’iyyar APC. Nayi haka ne saboda ya ni imani yafi Buhari har gobe.”
DABO FM ta tattaro cewa; Buba Galadima, ya kasance babban jigo a tafiyar shugaba Muhammadu Buhari tin daga shekarar 2003 har zuwa shekarar 2015.
Bayan samun nasarar shugaba Buhari a 2015, alakar Buba Galadima da Shugaba Buhari tayi tsamari akan shugabancin jami’iyya. Inda a 2019, Buba Galadima ya ja layi da shugaba Buhari, ya goyi bayan dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
