Labarai

Hukumomin Saudiyya sun sake maka dan Najeriya da aka yi wa cushen kwayoyin ‘Tramadol’ a Kotu

Rahotannin da suke iske DABO FM daga iyalan wani bawan Allah dan jihar Zamfara, Ibrahim Ibrahim Abubakar, sun bayyana mana yacce hukumomin kasar ta Saudiyya suka maka Ibrahim duk da hukunci Kotun Jidda tayi na wanke shi daga zargin shigar da wata jaka cikin kasar ai dauke da kwayar ‘Tramadol’

Idan ba’a manta a ranar 30 ga watan Afirilun 2019, hukumomin Saudiyya suka sake wasu ‘yan Najeriya ciki har da matashiya Zainab Aliyu bayan rashin samunsu da aikata laifin shiga cikin kasar da kwayar ‘Tramadol’ da kuma shigar gwamnatin Najeriya cikin lamarin.

Bisa ga takardun da muka tabbatar, an kama Ibrahim Ibrahim tin a daren ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2017, bisa umarnin hukumar hana fasa kauri da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, jami’an tsaron kasar ta Saudiyya sukayi awon gaba da Ibrahim zuwa ofishinsu domin gudanar da bincike. A inda ya bayyana musu cewar bashi da masaniyar jakar da kwayoyin suke ballantana ayi batun ya shigo dasu cikin kasar.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi suka cigaba da tsare Ibrahim domin gudanar da bincike akan zargin da akeyi masa. Hukumar ta fitar da takarda mai lamba 1703203, wanda ta tabbatar da samun kwayar ‘Tramadol’ kimanin 1497 a wata jaka mai dauke da sunan Ibrahim Ibrahim Abubakar.

Hakan yasa sun cigaba da tsare shi har zuwa ranar da aka aike dashi kotu domin fara gudanar da shari’a.

A wata takardar hukunci da kotun hukunta masu manyan laifuka dake Jeddah karkashin jagorancin mai shari’a Abdul’aziz Hassan Hassin Al-Maliki, mai lamba 39449020, ta wanke zargin da hukumar sha da fataucin miyagun kwayoyin kasar take yi wa Ibrahim Ibrahim na safarar kwayar ‘Tramadol’.

Iyalan sun shaida mana bayan hukuncin Kotu, hukumomin kasar sun sakeshi, sai dai sun hanashi takardun shi na dawowa gida Najeriya. Wanda a yanzu haka ya shafe watanni 6 basu bashi takardun da zai iya komawa Najeriya ba, sun kuma sake makashi a Kotu domin cigaba da gudanar da Shari’a.

Shin Ibrahim ya kai kokenshi ga ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Saudiyya? Shin wana yunkuri tayi domin ceton dan kasarta? Lamarin da DABO FM bata tabbatar ba, sai dai mun tuntubi ofishin a yau Alhamis domin ji daga gareshi a kan batun wanda muke tsumayin ji daga garesu.

Ibrahim Ibrahim Abubakar daya ne daga cikin malamai da gwamnatin jihar Zamfara da dauki nauyin zuwansu kasar Saudiyya domin yin Umara. – DABO FM bata tabbatar ba.

Masu Alaka

A tantance jami’an tsaro domin ana zargin akwai hannun su a hare hare -Sheikh Sani Jingir

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 169.74 don gyaran tituna 10

Dabo Online

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

2023: Akwai yiwuwar rugujewar APC bayan mulkin Buhari -Fayemi

Muhammad Isma’il Makama

Karfin wutar Lantarkin Najeriya ta ragu da 3,231MW

Dabo Online

A najeriya, an haifi Jarirai sama da 26,000 a daren sabuwar shekarar – UNICEF

Dabo Online
UA-131299779-2