Muhammad Dangalan
Bankin Muslunci na Jaiz ya bayyana samun ribar tsabar kudi na Naira biliyan 1.79 bayan kammala biyan haraji a shekarar 2019.
A wata sanarwar da bankin ya fitar, ya bayyana cewar ribar da bankin a samu a 2019 ya karu da kashi 114 wanda bankin ya samu a 2018.
DABO FM ta tattara cewar bankin ya samu ribar Naira miliyan 834.36 a shekarar 2018.
Haka zalika yawan kudaden da abokan huldarsu suka ajiye a bankin ya samu karuwa da kashi 50 daga biliyan 85.03 zuwa biliyan 127.193.
Bisa yadda bankin yake tafiyar da tsarin Shari’ar Musulunci, masu hannayen jari a banki zasu samu ribar kobo 6.06 a kowanne hannun jari a maimakon kobo 2.83 da suka samu a 2018, karin ribar ya karu da kashi 114.
Da yake jawabi a game da cigaban da bankin ya samu, babban daraktan bankin, Hassan Usman yace kokarin kyautatawa abokan huldarsu ne ya janyo samun ribar duba da “karuwar ajiyar kudin daga abokan huldarmu.”
