Labarai

Wani mutum ya shiga gasar cin kwai 50, ya mutu bayan cinye 41 akan N10,000

An bunkasa 1/05/2020.

Jaipur India: Wani mutum mai shekaru 42 dan asalin jihar Uttar Pradesh ta jihar Indiya mai suna Subhash Yadav ya rasa ranshi bayan yin gasar cinye kwai guda 50.

Rahotanni sun bayyana yadda mutumin ya karbi tayin gasar bayan da musu ya barke a tsakaninshi da wani a kasuwar Bibiganj wanda ta kai sun sanya rupee 2000 (N10,000) ga duk wanda ya iya cinye wa, kamar yadda jaridar TOI ta fitar.

Subash ya karbi tayin gasar tare da samun nasarar cinye guda 41, daga nan ne ya shide a kasa wanda hakan tasa mutane sukayi gaggawar kaishi asibiti inda anan ne yace ga garinku nan.

Likitoci a asibitin Kwalejin likitanci ta Sanjay Gandhi, sun alakanta mutuwar Mista Subhash da cin wuce iyaka. Sun ce yana raye har lokacin da aka kaishi asibitin inda bayan awanni ne a cewarsu ya mutu.

Masu Alaka

Gwamnatin kasar Indiya ta kaddamar da fara siyarda Audugar Mata akan Rs1 (N5.07)

Dabo Online

Indiya: Magidanta 1,774 ne suka kai karar matansu yayin dokar zaman gida a watan Afrilu

Dangalan Muhammad Aliyu

Jami’an Najeriya suna hana Likitoci a Indiya baiwa Zakzaky kulawar da ta dace

Dabo Online

Bidiyo: Gwamna a Indiya, ta kunyata ma’aikaci akan kashe N2550 ba bisa ka’ida ba

Dabo Online

Yadda Indiyawan Hindu sukayi wanka da cin kashin Saniya don magance Corona Virus

Dabo Online

Zaben2019: Wasu ‘yan Najeriya mazauna kasar Indiya, sun bayyana murnarsu ga nasarar Buhari

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2