Babban Labari

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga sun sace Sakataren Gwamnatin jihar Nassarawa

Da safiyar Yau Lahadi ‘yan Bindiga sukai a wun gaba da Sakataren Gwamnatin jihar Nasarawa, Mista Jibrin Giza, Kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Kwamashinan ‘Yan Sandan jihar, Mista Bola Longe ne ya tabbatar a faruwar lamarin, in da ya tabbatar da cewa ‘yan Bindigar sun kutsa gidan Sakataren ne da safiyar yau Lahadi a yankin Shabu na Lafiya babban birnin jihar, suka kuma yi awun gaba da shi.

Kawo wannan lokaci ‘yan bindigar ba su kira waya ko sun ce wani abu ba don gane da wannan lamari.

UA-131299779-2