Jaipur, India (DABO FM) – A sassan nahiyar Asia, yau Lahadi, 21 ga watan Yuni 2020, an samu kusufin Rana, kamar yadda masu hasashen masana yanayi suka ayyana.
Masanan sun ce za a samu ganin kusufin ranar a nahiyoyin Asiya, Afirka, Pacific, Tekun Indiya da wani bangare na Turai da Austiraliya.
DABO FM ta tattara yadda aka samu kusufin ranar a garin Jaipur na jihar Rajasthan da sauran sassan kasar Indiya da Hadaddiyar daular Larabawa.

- Yadda ta kasance a kasar Nepal
2. Yadda Rana tayi kusufi a birnin Delhi (Indiya)
3. Yadda Rana tayi kusufi a kasar Pakistan
4. Yadda Rana tayi kusufi a Hadaddiyar Daular Larabawa
Mene ne Kusufin Rana?
Kusufin wata yana faruwa a lokacin da Wata da Duniyar’Earth’ da kuma Rana, sannan inuwar wata ta lullube duniyar ‘Earth’.
Kusufin wata ya kan faru ne idan wata ya wuce ta tsakiyar rana da kuma duniyar ‘Earth a matakin sabuntaka, idan inuwarshi ta lullube duniya ya yin da yake wuce wa tsakanin Rana da Duniya.
