A yau shahararren mawaki Dokta Adamu Dan Maraya Jos yake cika sharu 5 da rasuwa, wanda ya koma ga Allah a ranar 20 ga Yunin 2015.
DABO FM tabi cikakken tarihin mawakin domin tinawa dashi bisa gudun mawar daya bawa harshen hausa, al’ada, zamantakewa, fadakarwa daya bayar. Kamar yadda aka wallafawa a WIKIPEDIA, An haifi Adamu Dan Maraya a shekarar 1946 a garin B’ukur da ke cikin jihar Plateau. Bayan rasuwar uwayensa, aka fara kiransa Dan Maraya (an orphan).
Cikin binciken da DABO FM tayi kafar DW ta bayyana Dr. Adamu Dan Maraya dai ya bar duniya ba tare da samun haihuwa ba, to sai dai ya rike yara marayu da dama da suka girma a hanun sa, daya daga cikin su shi ne Alhaji Kuchili Dan Maraya.
Mai shekaru 69 da haihuwa a duniya, marigayin ya ziyarci kasashen duniya dabam- dabam sanadiyyar wakokinsa masu bada fuskanta game da zaman lafiya, hadin kan jama’a dama ilimantarwa kan sha’anin zamantakewar bil Adama.
Marigayi Dan maraya dai ya sami lambobin yabo da dama daga ciki da wajen Najeriya sabili da irin kwarewarsa wajen tsara wakokin da ke zamantowa tamkar karatu ga me saurare.
Dr. Adamu Dan Maraya dai ya bar duniya ba tare da samun arzikin haihuwa ba, to sai dai kuma ya rike yara marayu da dama da suka girma a hanun sa, daya daga cikin su shi ne Alhaji Kuchili Dan maraya.
Mai dakin Dr. Adamu Dan Maraya jos, Hajiya Hafsatu ta ce marigayin ya rike ‘ya’yan da ke hanun sa marayu tamkar shi ya haife su.
Wasu abokan sana’ar Dr. Adamu Dan Maraya da suka hada da maroka, da mawaka, sun sheda cewar babu wata gaba ko kuma rashin jituwa da ake samu da shi a duk tsawon lokaci da suka yi suna tare da shi.
Alh, Mohammadu Baka rainuwa, wani fittacen sankira ne da suka yi zaman lafiya da marigayi har kusan shekru 60, ya tabbatar da hakan.
Hakan nan wasu da suka shedi halayen marigayi Dan Maraya Jos, mutane irin su Shehu Abdulkadir wanda akafi sani da ( Sardauna ) ya siffanta Dan Maraya matsayin matum mai kyauta da son jama’a har ma da dabbobi.
Dr. Dan Maraya Jos dai ya yi wakoki masu tarin yawa, to amma wakar da ke zamantowa karatu ga al’umma a koda yaushe, ita ce wannan wakar da ya yi mata lakabi Mutuwa Rigar kowa.
Kaɗan daga cikin waƙoƙinsa su ne:
- Auren Dole
- Gangar Ciki
- ɗan Adam
- Talakawa
- Mai Akwai Da Babu
- Waƙar Sana’a
- Gangar Malamai
- Siyasa
- Haƙuri
- Malalaci
- Duniya
- Ina Ruwan Wani
- Isahara
- Waƙar Aure
- Bob Guy
ɗan Maraya ya yi suna kwarai a arewacin Najeriya, Nijer, Ghana da Kamaru. Yawancin waƙoƙin ɗan Maraya suna bayani ne a kan al’amurra na yau da kullum da ke fuskantar mutane a ƙasar Hausa. Muna addu’ar Allah ya gafarta masa.
