Home Labarai‘Ya kamata a rika maimata Kayan Lefe duk bayan shekara 5’

‘Ya kamata a rika maimata Kayan Lefe duk bayan shekara 5’

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments
Kayan Lefe

Jaipur, India (DABO FM) – Tun farkon makon da muke fita daga ciki, akayi ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta akan Kayan Lefe da maza suke yi wa matan da zasu aura a kasar Hausa.

Kamar kowacce muhawara akan samu masu goyon baya da wadanda suke barranta.

A bangaren masu nuna rashin goyon bayan soke Lefe, wasu daga ciki sun kirkiri maudu’in #TeamLefeDole, wadanda a cewarsu idan za a soke lefe, lallai ne maza su rika yi wa mata kayan daki da na kitchen.

A gefe guda kuma masu so a soke lefe sun dora lefe a matsayin wani jigon tsari dake hana matasa yin aure sakamakon wahalar da take ciki.

DABO FM ta tattaro wasu daga cikin ra’ayoyin da aka bayyana wadanda suka fi daukar hankali kamar haka;

Fatima Bala Mukhtar, ta ce; “Ya kamata duk bayan shekaru biyar fa a na maimaita lefe!
To wanda ka yi sun kare… Don haka mata aradu kar mu manta.”

Yakubu Musa ya ce; Shi fa lefen nan tunda mu za mu mora a hade shi da kayan daki duk a dora mana. Batun gaskiya ai mu za mu hau kujerar, mu za mu ci a plates din. Yar ma da aka ba mu ai ta isa. Allah ya sakawa masu yaya mata an dade ana dora muku wahala.

Naseeba Babale: “Kar ku tara na lefe kun ji, ku yi ta kashewa a data.”

A bangaren masu goyon bayan soke lefe kuwa, DABO FM ta yadda suka suka bayyana nasu ra’ayoyin.

Bin Ladan Mai Littafi, ya ce; “Tsadar aure; arhar zina. Mafi albarkar aure, mafi sauƙinsa wahalhalu. LEFE: Jalauta jari, ko talauta jari, riba, ko asara?

A gefe guda kuwa, akwai wadanda suka mayar da muhawarar kamar taskar nishadi domin yin raha da rage lokaci. DABO FM ta gane cewa suna sane cewar ya zame musu tilas suyi kayan lefe a lokacin da za suyi aure, sai sai bakin da Allah Ya tsaga, ba Ya hanashi abinci.

A wani labarin kuma, wata mai fashin baki akan al’amuran yau da kullum, Zainab Muhammad Michika ta ce; ‘Da ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, da mata sun riƙa aura wa maza ƙawayensu’

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00