Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin hukumar tsara birane ‘KASUPDA’ ta rushe gidaje sama da guda 50 a karamar hukukar Zariya.
Gidajen sama da 50 da aka gama da wadanda ba a gama, an wayi gari an rushe gidajen da suke a yankin Kwagwaro, filin da ake sallar Idi wanda ake masa lakabi da filin Idin Bare-bari da ke kan hanyar Kofar Kona zuwa Kofar Gayan a karamar hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.
Rusau din da aka fara tun a Litinin da ta gabata, inda mutanen yankin suka ce sun wayi gari an sa masu alamar fentin umarnin su kawar da gidajen su daga wurin kuma ba tare da ba su rubutacciyar takarda daga hukumar tsara birane ta Jihar Kaduna wato KASUPDA ba.
Baya ga nan, “a safiyar Laraba, Jami’an hukumar KASUPDA da rakiyar Jami’an tsaro suka zo suka cigaba da aikin rusa gidajen da ke wurin, duk da daga bisani sun dakatar kuma suke ce sun bai wa mutanen da suke zaune a gidajen su umarnin kwashe kayayyakin su, wanda suke zargin an gina su ba bisa ka’ida ba.” – cewar wani mazaunin yankin a zantawarshi da DABO FM.
‘Mamallaka’ filin, Bare-barin Zazzau, sun zargi wasu da suka ce marasa kishin kasa ne suka yayyaka filin kuma suke siyarwa ba tare da izininsu ba, hakan ya sa ake zarginsu da kai korafi wajen hukumar wadda ta dauki matakin rushe ginin da akayi a filin.
Sai dai manema labarai sun tuntubi hukumar KASUPDA ciki har da DABO FM da su ne aka ga ma’aikatar su na jagorantar rushe gine-ginen, Mai magana da yawun hukumar a Jihar Kaduna Nuhu Garba Dan Ayamaka, ya bayyana cewar tun da jimawa hukumar su ta dade tana gargadin mutanen yankin a kan su guji cigaba da gine-gine a wannan wajen, saboda a cewarsa fili ne na Idi, ba a bawa kowa ba domin gudanar da aiki a filin.
Shiyasa yanzu da masu filin suka bukaci abun su sai ta sa ala tilas suka dauki wannan matakin.
