Home LabaraiA gaggauce: Buhari ya amince da dakatar da Magu, ya yi nadin sabon shugaban rikon EFCC

A gaggauce: Buhari ya amince da dakatar da Magu, ya yi nadin sabon shugaban rikon EFCC

by Dabo Online
0 comments

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Ibrahim Magu, tsohon shugaban riko na hukumar yaki da yi wa kasa ta’annati, EFCC.

Haka zalika shugaban ya amince da nadin Muhammadu Umar a matsayin sabon shugaban riko na hukumar.

Gwamnatin Najeriya ta ce dakatar da Magu zai bayar da damar bincikar Ibrahim Magu daga zarge-zargen da ake yi masa na yi cin hanci da rashawa, ba tare da samun tsaiko ko kuma tasgado ba.

Abubakar Malami, ministan shari’a na Najeriya ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Umar Gwandu ya fitar a ranar Juma’a.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00