Amsar tambaya tare da Sheikh Yusuf Ali
Tambaya: Dr. Shin wake-waken yabon Manzon Allah, (sallallahu alaihi wa sallama,) da ake ta yi da kayayyakin kade-kade na zamani, ya halasta a Musulunci? Daga Zainab Shehu Mahuta, Katsina.
Amsa: Malamai sun yi bayanin irin abubuwan kade-kade da bushe-bushe, sun bayyana nau’in da ya halatta da wanda bai halatta ba, kamar yadda ya zo a littafin Mukhtasar Khalil da sharhunan sa a babin Walima.
Daga cikin sharhunan Mukhtasar, akwai littafina na digiri na biyu, mai suna: (Kifaayatud Dullaabi Fin Nikaahi) wanda aka daga darajar sa zuwa digiri na uku (Ph.D.) a shekarar, 1993, shafi na 47. Na kawo misalan wasu kayayyakin kida, kamar; ad-duff da al-ghirbaal da ad-daar, duka suna nufin bandiri da duk wata ganga da aka rufe bangarenta daya aka bar dayan a bude.
Malamai sun hadu akan ana son amfani da su a abubuwa na farinciki, kamar bukukuwan aure da suna da irinsu, ba sabani. Amma abin kidan da aka toshe fuskokin sa biyu, kamar; “Kabar “ kalangu da “mizhar” wata iriyar ganga kamar Kalangu, amma mai kusurwa hudu, da irinsu, wasu malamai sun ce sun halatta, wasu sun ce makaruhi ne, amma abubuwa busa, kamar kaho “buuq” ko sarewa, “ zumarah” da irinsu, su ma sun halasta.
Amma abubuwan kida masu tsirkiya, kamar kuntigi da goge da garaya molo da makamntansu, ra’ayin mallamai ya saba game da halacci ko haramci, wasu sun ce haramun ne, yayin da wadansu suka tafi a kan halas ne. A Wannan shi ne karshen bin da na rairayo daga littafin nawa.
A sani na mawakin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallama) dake Kanon Dabo, Alhaji Sharif Rabi’u Uthman Baba, shi ne ya bullo da wannan sabon tsari na sirka yabon Annabi Muhammad, Mai tsira da Amincin Allah, kamar shekaru goma da suka gabata. Dangane da caa da akayi masa saboda da wannan sabon salo, ta sa, shi kansa, da wasu jama’a da dama, masu kishin Addini, sun ta neman fatawar wannan lamari da ya daure musu kai, ta shirye-shiryena na kafofin yada labarai, ko a gida ko a wuraren da nakan ba da karatu.
Zuwa yanzu dai ga matsayina a wannan masa’ala: Amfani da kade-kade a bukukuwa na farin ciki, in dai babu cudanya tsakanin maza da mata, ya halatta. Abin da yake karfafa wannan matsayi nawa kuwa shi ne abin da Hujjatul Islami, Al-Imamul Ghazali, a littafinsa (al-Murshidil Mubin) inda ya ce:(wake-wake da kade-kade a biki na aure ko walima ko suna da irinsu, sun halatta, saboda zasu motsa abubuwan da za su kara habaka farin ciki na halas ko ma wanda shari’a take bukata. Saboda abin da ya zo daga sayyidatina A’isha (RA) cewa Sayyidina Abubakar (RA) ya je gidan ta, sai ya sami wasu ‘yanmata guda biyu suna kida suna waka, da Babbar Salla, a lokacin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallama) ya lulluba da tufafin sa, sai Sayyiduna Abubakar ya tsawatar musu, sai manzon Allah ya bude fuskar sa yace: Abubakar! ka kyale su mana, ai kwanukan farinciki ne! [Buhari da Muslim suka ruwaito] a duba Sirajus Saliki, 2/66.
Wasu hujjojin kuma sun hada da: tarbar da ‘yammata suka yi wa Annabin Rahama lokacin da ya shiga Madinah yayin da yayi kaura zuwa can, suka tarbe shi da kade-kade da wake-wake na yabon Annabi, (Sallallahu Alaihi Wa Sallama.) An ce wata rana mata ‘yan kai amarya za su kai wata yarinya da aka ce Nana A’isha ce rike ta, har za su tafi sai Manzon Allah ya ce: ku tsaya, ya zaku tafi da amarya haka sulu, ba kida ba waka?! Ai Ansar suna son wasanni, sai suka ce: to me za mu rinka cewa? Sai ya ce: ku rinka kida kuna cewa: Mun zo muku, mun zo muku. Ya gaishe mu, ya gaishe ku. Da badon jar alkama ba, ‘Yan matan ku da ba su yi kiba ba. Da ba don jajayen kudi ba, da bata zauna a wajen ku ba.
Haka an ce Annabi mai tsira da Amincin Allah yakan yi wa Nana A’isha izinin kallon wasannin Habashawa da sukan yi a Masallacin sa.
Abin da ya gabata yana nunin halaccin yabon Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallama) da kade-kade da bushe-bushe, na zamani musamman wadanda suke da siffofin da muka ambata a baya, kuma da nufin kara zaburar da musulmi don su kara son Annabi da Musulunci, kuma ba wani abin munkari da sabawa Allah Ta’ala da gurin ya kunsa, kamar cakuda tsakanin maza da mata, da saurasu. Wallahu A’lam.
