Wasu fusatattun matasa sun cinna wa motar Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) wuta bayan wani hatsari da ya faru a yankin Kwanar Dawaki da ke Kano.
DABO FM ta tabbatar da cewar lamarin ya faru ne bayan wasu fusatattun matasa sun zargi jami’an hukumar Karota da haddasa haɗarin.
Da ya ke tabbatar da faruwar al’amarin, mataimakin shugaban hukumar Karota, Auwal Shu’aibu, ya musanta zargin da a ke yi wa hukumar, ya ce lamarin ya faru ne a ƙoƙarin jami’an hukumar na kama direbar tirela da ya buge mota ƙirar sharon.
Ya ce hatsarin ya samo asali ne bayan wata babbar motar tirela ta buge wata mota ƙirar Sharon, lamarin da ya haifar da hatsari.
A cewarsa, jami’an KAROTA sun yi yunƙurin kame direban motar tirelar ne domin gudanar da aikinsu, sai dai wasu fusatattun matasa su ka afka musu tare da cinna wa motar hukumar wuta.
Matasan sun yi zargin cewa jami’an KAROTA ne suka haddasa hatsarin, amma hukumar ta musanta wannan zargi, tana mai cewa jami’anta sun isa wurin ne domin daƙile lamarin da kuma aiwatar da doka.
