Rahoton da ya nuna cewa Gwamnatin Jihar Kano ta kashe kusan Naira biliyan 26.5 wajen gudanarwar gidan gwamnati, ofishin gwamna da kuma tafiye-tafiye a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026 ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar jihar.
Jaridar PUNCH ta ce bayanan da ta tattara daga rahotannin aiwatar da kasafin kuɗin jihohi sun nuna cewa Kano ta kashe Naira biliyan 25.87 wajen gudanar da gidan gwamnati da ofishin gwamna a cikin watanni shida na farkon shekarar.
Baya ga wannan, an kashe karin Naira miliyan 626.95 kan tafiye-tafiye da sufuri na gwamnati, abin da ya kai jimillar kuɗin zuwa kusan Naira biliyan 26.50.
Duk da cewa adadin kudin da aka kashe kan gidan gwamnati da ofishin gwamna ya ragu idan aka kwatanta da shekarar 2025, inda aka kashe Naira biliyan 28.84, zuwa yanzu an kashe Naira biliyan 25.87 a farkon rabin shekarar 2026.
Wannan na nufin an samu raguwar kusan Naira biliyan 2.98, kwatankwacin kashi 10.32 cikin 100.
Sai dai rahoton ya jaddada cewa kudaden ba albashin gwamna ba ne, kuma ba wai kudin da gwamna ya kashe da kansa ba ne.
A cewar rahoton, kudaden sun haɗa da gudanar da gidan gwamnati da ofishin gwamna, albashin ma’aikata, kula da gine-gine, tsaro, ayyukan hukuma da sauran abubuwan da suka shafi tafiyar da bangaren zartarwar jihar.
Haka kuma, Naira miliyan 626.95 da aka ware a bangaren tafiye-tafiye ya shafi sufuri da tafiye-tafiyen gwamnati.
Rahoton ya ce yawan kuɗaɗen da aka kashe, duk da raguwar su daga shekarar da ta gabata, ya sake bude batun yadda ake amfani da kudaden gwamnati wajen gudanar da manyan ofisoshin siyasa.
Binciken PUNCH ya kuma nuna cewa jihohi 33 da aka samu bayanansu sun kashe jimillar Naira biliyan 512.10 kan gudanar da gidajen gwamnati, ofisoshin gwamnoni da tafiye-tafiye a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026.
