Dino Melaye, Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, yayi kira ga hukumar ASUU data fara binciken kwa-kwaf akan takardun Farfesoshin da sukayi aikin zabe.
Ya godewa hukumar zabe ta INEC bisa yadda yacce tayi kokari wajen nunawa duniya Farfeshoshin da suke kasa yin lissafin da yara ‘yan Firamare suke iya yi cikin sauki.
Daga karshe yayi kira ga hukumar ASUU data kirawo Farfesoshin da sukayi aikin zabe domin tantance sahihanci da nagartar kwalin karatunsu.
I appreciate INEC for exposing some of our Professors who could not solve mere arithmetic that a primary school pupil will solve. ASUU should be concerned and call to order the qualifications and integrity of these idiotic professors. – SDM
— Senator Dino Melaye. (SDM) (@dino_melaye) March 26, 2019