//

Abubuwan da suka faru a Rana Irin ta Yau, 28 ga Satumba a fadin Duniya

dakikun karantawa

A ranar 28 Satumbar 1992 Jirgin Sojojin Najeriya yayi hatsari a kusa da Jihar Lagos, inda mutane 163 suka rasu.

A ranar 28 ga watan satumban shekarar 2018 Hukumar Jin ‘Kai ta Najeriya ta kaddamar da kudi dalar amurka $17,700,000 domin ceton rayukan mutanen Arewa Maso Gabas daga mawuyacin halin da suke ciki sakamakon hare-haren yan kungiyar Boko Haram.

A ranar 28 ga watan Satumban shekarar 1538 Babban Jirgin Ruwan Yaki na Daular Usmaniyya karkashin jagorancin Barbaros Hayrettin Pasa ya nutsar da jirgin ruwan Rundunar Krista a kusa birnin Preveze dake Girka.       

Haka kuma a ranar 28 ga watan Satumbar 2003 ‘Kungiyar ‘Kwallon ‘Kafa ta Mata ta Najeriya tasha kashi a hannun ‘Kungiyar ‘Kwallon ‘Kafa ta Sweden daci 0-3 a gasar cin Kofin ‘Kwallon ‘Kafa ta Duniya.

A ranar 28 ga watan Satumban shekarar 1864 aka kafa Kungiyar Ma’ikatan Kasashen Waje a birnin Landan.

A ranar 28 ga watan Satumban shekarar 1970 Jamal Abdul Nasir ya rasu bayan ciwon zuciya ya kamashi wanda ya shahara da kishin kasashen larabawa inda kuma shi ne ya kafa Kasar Siriya da Hadaddiyar Daular Larabawa sannan shi ya mulki kasar Masar har tsawon shekara 14. 

A ranar 28 ga watan Satumban shekarar 1989 Tsohon Shugaban Kasar Filipin Ferdinand Marcos ya rasu a Jahar Hawai dake Amurka wanda shi ya mulki Filipin a tsakanin shekarar 1965 zuwa 1986. Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasar ya saci miliyoyin Dala yayinda ya yi mulkin danniya a kasarsa.

A ranar 28 ga watan Satumban shekarar 1994 wani jirgin ruwa mai suna “Estoniya” ya nutse Tekun Baltic inda mutane 852 suka rasu. 

A ranar 28 ga watan Satumban shekarar 2016 Shugaban Kasar Isra’ila Simon Peres ya rasu wanda ya yi musu da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wani taro da aka yi a Davos. A taron ne Erdogan ya yi wa Shugaban kasar raddi da cewa, 
“babu wanda ya kai ku iya kisa. Mun san cewa kun sha kashe yara a gabar teku”.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog