Home LabaraiBabban LabariDole kowa ya bada tashi gudunmuwar domin dakile yaduwar fyade a kasar nan – Habiba Muhammad

Dole kowa ya bada tashi gudunmuwar domin dakile yaduwar fyade a kasar nan – Habiba Muhammad

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

An bayyana matsalar karuwar samun masu aikata fyade a matsayin babbar damuwa da ke kawo tarnaki ga cigaban al’umma musamman tunda yanzu ba mata kadai ba har da maza ake cin zarafin su.

Shugaban wata gidauniya da ke rajin kula da ilimin ‘ya’ya mata mai suna Center For Girls Education a turance Hajiya Habiba Muhammad, ta bayyana hakan a zantawar ta da Manema labarai a Zariya ta Jihar Kaduna. ta ce akwai abun takaici da sau da yawan lokuta ake kokarin boye wanda suka aikata laifin fyade ba tare da mika su ga hukuma domin daukar mataki ba, inda ta bayyana hakan a matsayin babbar matsalar da ke kara ta’azzara lamarin.

A cewar ta idan aka bar wannan abun ya cigaba da tafiya, to babu makawa za’a gurbata al’umma baki daya.
Kuma ba mafita bane da za’a daura al’umma a kai.

Ta bayyana tunkarar matsalar a matsayin wanda kowwa zai zo a hadu a hada karfi da karfe tun daga bangaren iyaye da hukuma da Sarakuna da kuma bangaren shari’a domin samun nasarar kawar da irin wannan matsalar.

“Na san akwai wacce aka taba ma fyade ta samu ciki, da aka zo auren kanwar ta sai aka fara bincike irin na auren nan, daga karshe cewa aka yi kada a auri kanwar, duk da ba ita ce aka yi wa fyaden ba”, a cewar Habiba Muhammad.

Daga nan sai ta yaba ma gwamnatin Jihar Kaduna saboda matakan da take dauka na rashin sassauci ga duk wanda aka samu da laifin aikata fyade, kuma ta yi fatan sauran jahohi su yi koyi da Jihar nan wurin tabbatar da ganin ana hukumta masu fyade da sauran laifuka na yau da kullum

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00