Najeriya

An kai hari Jami’ar Maiduguri

A daren jiya Lahadi wayewar yau Litinin wasu mahara dauke da muggan makamai suka kai hari jami’ar Maiduguri.
Maharan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne, sun shiga makarantar wajen karfe 10:00 na dare. Maharan sun shiga da ababen hawa kimanin Guda 10. Sun yi ta harbe-harbe cikin iska, kafin daga bisani Sojoji su fatattake su.

Bayan tafiyar Maharan, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci Jami’ar a daren na jiya.

Comment here