Zabe: Gwamnan jihar Bauchi ya baiwa masu saka ido a zabe cin hanci, don su kau da kai

dakikun karantawa

Gwamnan jihar Bauchi, Barrister Muhammad Abubakar ya baiwa masu saka ido akan zabe cin hanci domin su kautar da idonsu bisa shirin yin magudi ta hannun sakataren jami’iyyar APC na jihar Bauchi.

Jaridar Wikki Times ta rawaito cewa, Kwana daya kafin zabe, Sakataren jami’iyyar APC na jihar Bauchi, Alhaji Bako Hussaini,  ya tantance masu sa idon a babbar sakatariyar jami’iyyar dake By-Pass na Maiduguri. Kowane jami’i na bada kwafin takardar da hukumar INEC ta bashi domin tabbatar sa sahihancin kasancewa “Mai sa ido a zaben.”

Yayin tantancewa.

Binciken da Haruna Abdullahi ya gudanar, ya gano yadda masu saka idon suka mikawa jami’iyyar APC wuya wajen yin amfani dasu a zaben 2019 da aka gudanar baki daya.

Jami’iyyar APC ta baiwa masu saka ido na cikin gida kimanin N100,000 zuwa N250,000 a zaben shugaban Kasa tare da bada kudi irinsu a zaben Gwamna. – Kamar yadda Jaridar Wikki Times ta rawaito hadi da Sahara Reporters.

Jami’iyyar bata tsaya nan ba, ta kama musu dakunan kwana guda 45 na tsawon kwana 4 a Chaba Guest Inn Bauchi a lokacin zaben Gwamna da ‘yan majalissun jiha.

Jaridar Wikki, ta bankada wani hoto a dai dai lokacin da Agent din jami’iyyar APC yake mikawa wani daga cikin masu saka idon zunzururun kudade a cikin mota.

Sakataren jami’iyyar ta APC ya baiwa masu saka idon kudin (N100,000 zuwa N250,000)) a zaben shugaban Kasa, ya bada kudin ne a kungiyanci, yadda tsarin raba kudin ya kasance shine, iya girman kungiya iya yawan kudinta. A yayin da kuma a zaben Gwamnoni, jami’iyyar ta aike agent dinta mai suna “Malam Ya’u” domin rabon kudin.

A ranar da agent din zai bawa wani daga cikin jami’an sa idon N100,000 bayan an kammala zaben Gwamna, ranar 16 ga watan Maris, 2019, an hangi Malam Ya’u tare da wasu mutanenshi a Container dake da zama a Kasuwar Wunti, kusa da Filin Wasa na Bauchi Multipurpose da misalin karfe 3:01pm a  mota koriya, kirar Honda Civic mai lamba AH 495 KTG Bauchi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog