KANO: CP Wakili ya dawo bakin aiki bayan tafiyar DIG Ogbizi

Karatun minti 1

Kwamishinan ‘yan sandar jihar Kano, CP Muhammad Wakili ya dawo bakin aiki, na kasancewa shugaban rundunar ‘yan sandan jihar Kano, jim kadan bayan tafiyar DIG Anthony Micheal Ogbizi daga jihar ta Kano a matsayin  jami’in da rundunar ‘yan sanda ta turo domin kula da zaben da bai kammala ba na Gwamna a Kano.

Kwanaki kadan dai rundunar ta turo wasu manyan jami’an ‘yan sanda domin tabbatar da gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali.

Sai dai kungiyoyi dayawa na ganin zaben da aka gudanar ba zabe ne da akayishi bisa ka’i’da ba, duba daga yadda akayi magudin zaben da kuma hana jama’ar garin yin zaben ba.

Lamarin daya tada hargisti da tarzoma a fadin jihar Kano a lokacin gudanar da zaben.

 

Kalli bidiyon yadda ‘yan sanda suka tari CP Wakili lokacin daya iso wajen aiki.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog