Biyo bayan rahoton Aminu Ado Bayero ya tsige jigo a jihadin Shehu Bn Fodio wanda ya nada marigayi Ado Bayero sarki da muka fitar, mutane da dama suna ganin babu hadin Sarkin Bai da jihadin Shehu Usman.
DABO FM ta kara binciko kyakkawar alaka dake tsakanin Sarkin Bai da Shehu Usmanu.
Ana samun sarautar Sarkin Bai daga kabilar Dambazawa, wadanda su kuma sun kasance Fulani yan asalin kasar Senegal kamar yacce Ado Ahmad gidan Dabino ya wallafa a littafinshi mai take “Jagora Abun Koyi – Alh Mukhtar Adnan” wanda ya wallafa a shekarar 2003.
Daga kasar Senegal, Dambazawa sukayi ta yawon kiwo wanda ya kai sun rassa dayawa a kasashen Mali, Nijar, Chadi da Kamaru. Sun shafe kusan karni 2 da fara tafiye-tafiyensu wanda sukan tsaya a gari, su kiwata Shanunsu, sunyi kasuwanci kuma bayar da addinin Musulunci.
Bayan cika karni 2, sun shiga garin Borno kafin daga bisani suka sake wucewa garin Damban (Bauchi) a farkon karni na 16. Daga nan ne suka shiga Kano (Bangaren Jigawa a yau) kafin daga bisani suka kara shigowa gabashin Kano, garin Dambazau a yau (Karamar hukumar Takai).
Sun dauki lokaci mai tsawo kafin su cigaba da tafiya ta kudanci domin kauracewa shiga cikin garin Kano , kimamin nisan kilomita 21.
Bayan sun samu dauwamammen wajen zama a Kano lokacin da suka karbe ikon alkaryar inda suke a shekarar 1806 (Bayan yakin Kano da Shehu Usmanu), sun mayaye gidan Sarkin Bai dake kusa da kasuwar Jakara. Wasu daga cikin ‘yan Kabilar sun cigaba da yin yado zuwa wasu sassan wajen kasar ta Kano.
“Duk inda suka zauna, suna bawa wajen sunan Dambazawa.”
Shugaban kabilar Dambazawa na wancen lokacin, Modibbo ya kasance daga cikin daliban Shehu Usman Dan Fodio wanda bayan dawowarshi gida, ya tara mutanen kabilar domin yi wa shugabancin Shehu mubaya’a tin kafin yakin Shehu da Sarkin Gobir.
A lokacin da Shehu ya nufo yakin garin Kano, kabilun Sullubawa, Dambazawa, Yolawa, Jobawa da Hausa sun goya masa baya tare da taimaka masa wajen yakin.
Kabilar Dambazawa ta Sarkin Bai ta tara wa Shehu dukkanin dakarun yakinta a arewacin masarautar Kano (garin Dambatta) na tsawon kusan shekara guda kafin ayi gumurzun da aka karbe Kano.
- Kabilar Sarkin Bai (Dambazawa) sun kasance wadanda suka tsara yakin da Shehu Usmanu yaci garin Kano da yaki.
- Sun bawa Shehu gudumawar dakarun yaki masu yawan gaske wadanda suka tarasu a garin Dambatta a yanzu.
- Sun yi wa Shehu Mubaya’a (Duk da dama su Musulmai ne) tin kafin ya nufo garin Kano da yaki kasancewar shugaban Kabilar ya kasance dalibin Shehu Usmanu
