//
Thursday, April 2

Zamu yanke wutar da muke baku idan baku biya kudi ba – Najeriya ta fada wa Nijar, Togo da Benin

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin tarayya Najeriya ta alkauranta yanke wutar Lantarki da take bawa kashen Nijar, Togo, da Benin idan har basu biya bashin da ake binsu na dala miliyan 16 ba.

Shugaban kamfanin rarraba wutar lantarkin Najeriya, TCN, Usman Muhammad, shine ya bayyana haka tare da cewa bashin da Najeriya take bi ya kai kimanin dalar Amurka dubu 100.

“A lokacin da na zama shugaban wannan kamfanin, Najeriya tana bin kasashen Benin da Togo bashin dala dubu 100.”

“Sun biya wani abu daga cikin abinda suka sha, wanda ya kama har yanzu muna bin kasar Benin dala miliyan 14. Ita Nijar ta biya kusan nata duka, ana binta kasa da dala miliyan 2.

Masu Alaƙa  Sadiya Umar Faruq ta karyata shafin Twitter da yace babu batun Aurenta da Shugaba Buhari

DABO FM ta tattaro cewa shugaban kamfanin yayi barazanar yanke wutar Lantarkin kasashen idan har basu kammala biyan kudaden da ake binsu bashi ba, bisa matsayar da aka cimma.

“Zamu yanke musu wutar suma kamar yacce muke yanke wa anan.”

“Wutar Lantarki fa ba sadaka bace da mutane zasu sha kuma su kyalemu haka.”

Ya jaddada cewa zuwa yanzu ma an kai ga sa musu takun-kumi tare da rage samar da wutar har sai sun biya bashin da ake binsu.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020