Labarai

Babban shehin malamin coci ya samu wahayin El-Rufa’i bazai taba mulkin Najeriya ba

Babban Limamin Darikar Angilikan na Mabiya addinin Kirista da ke Garin Zariya, Abiodun Ogunyemi, ya sake yin magana game da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Rahoton Dabo FM na Jaridar Legit ya bayyana cewa Shehin Malamin Kiristan ya sake fada cewa babu yadda za ayi Malam Nasir El-Rufai ya zama shugaban kasa a Najeriya.

A cewar Malamin Ubangiji ne ya nuna masa wannan ba kowa ba.

Da ‘Yan jarida su ka tambayi Rabaren Abiodun Ogunyemi, a kan abin da ya sa ya ke bada tabbacin El-Rufai ba zai yi mulki ba sai ya ce: “Ba daga ni bane, na ba ku misalai, kuma su na nan da yawa.”

“Mutane kan dura a kai na a kan irin haka. Ba na damuwa. Lokacin da, na fito na ce Goodluck Jonathan ne matsalar Najeriya kuma ba zai kai labari ba. Ba ni ba ne, Ubangiji ne ya fada mani.”

Don haka wannan Malami ya ja hankalin Nasir El-Rufai ya hakura da batun neman shugaban kasa.

Ogunyemi ya ce ya taba fadawa Mabiyansa Abiola ba zai yi mulki ba, kuma haka aka yi.

Ya ce: “Idan aka nada ka Bishof, ofishinsa na dauke da aikin Malanta da kuma karamomi. Ban san sauran Limamai ba, amma ni tun da na zama Bishof, Ubangiji ya kan kunsa mani magana.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin Kaduna zata daukaka kara akan izinin Al-Zakzaky na zuwa Indiya

Dabo Online

Zaben Gwamna: El-Rufa’i na jami’iyyar APC ya lashe zaben gwamnan Kaduna karo na biyu

Yadda Hakimin Birnin Gwari ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutane suna tsaka da barci

Muhammad Isma’il Makama

KADUNA: El-Rufa’i ya ruguje dukkanin Jami’an Gwamnatin Kaduna

Dabo Online

Mallam El-Rufai ya kama malamai 2 da suka karya dokar hana fita

Dabo Online

Gwamnatin Kaduna ta shirya yiwa Dawakai 1000 allular rigakafin kamuwa daga Zazzabin Dabbobi

Dabo Online
UA-131299779-2