(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

An yi kiran tsige mai riƙon muƙamin daraktan cibiyar sarrafa fatu da kimiyya da kuma fasaha ta NILEST Zariya saboda kawo daidaito

dakikun karantawa

An nuna bukatar da ke akwai ga gwamnatin tarayya ta tsige daraktan riko na makarantar sarrafa fatu da kimiyya da kuma fasaha wato Nigeria Institute of leather and science technology samaru Zariya, saboda wuce ka’idar zama daraktan riko na makarantar.

Yanzu haka dai daraktan rikon Dakta Eucharia Ngozi Oparah ta kwashe kusan shekaru Uku tana matsayin daraktan riko, wanda ya saba wa ka’idan adadin watanni Shida da ke kumshe cikin dokokin aiki.

Wasu al’ummomi da suka kira kan su ‘Concerned Zaria Youth’ reshen jihar Kaduna suka bayyana bukatar tsige daraktan lokacin wani taron manema labarai da suka kira domin nuna damuwa kan tsawon lokacin da ta dauka tana jagorantar makarantar, wanda kuma hakan ya kawo cikas da koma baya ga cigaban karatu da gudanarwar Cibiyar.

Sun bayyana cewa, a baya sun yi rubuce-rubuce game da korafin nasu kuma suka tura ga ofishin Antoni Janar kuma ministan shari’a na kasa da sauran hukumomin da suke da ruwa da tsaki a kai. Sai dai har zuwa yanzu ba su samu wani cikakken bayani da zai gansar da su ba game da cigaba da kasancewar daraktan a madafun iko.

Cikin wata takarda dauke da sa hannun shugaba da sakataren kungiyar Imrana M Sani da Bashir Ibrahim bomo ta bayyana cewa Dakta Eucharia Ngozi, tana matsayin mai rikon muƙamin shugaban makarantar ne tun watan Yuli shekarar 2017.

Wanda kuma hakan ya saba wa ka’ida da tsarin aiki, musamman ko domin rashin sanya hannu a takardar shaidar kammala karatun dalibai da suke gama makarantar.

Saboda a doka ma sai cikakken daraktan ne zai iya sanya hannu kan dukkanin takardun dalibai masu kammalawa.

Sanarwar ta bayyana cewa, akwai wasu zarge-zargen da aka jima ana yi a makarantar da suka hada da ɗaukan ma’aikata ba bisa ka’ida ba da kuma nuna banbanci wurin daukar aiki.

Sai dai da manema labarai suka tuntubi hukumar makarantar domin kare kan su game da zarge-zargen da ake masu, magatakardan makarantar Mista Yohanna Yunana Midad ya musanta cewa mai rikon muƙamin daraktan makarantar na zama ba bisa ka’ida ba, tunda a cewar sa ba ita ta naɗa kanta a matsayin shugaban riƙon ba.
Kuma game da batun daukar ma’aikata ba bisa ka’ida ba, Yunana Midad, Ya ce tun da Dakta Eucharia Ngozi ta zama jagoran makarantar ba’a dauki karami ko babban ma’aikaci da yake aiki da ma’aikatan ba yanzu haka.
Sai dai ya yaba ma kungiyar da ta dauki ragamar rubuta korafin da ya ce daman doka ta basu daman gudanar da bincike kan abin da basu aminta ko kuma gane take-taken shi ba.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog