Wasu matasa sun cilla matar da suka caccakawa wuka bandaki, suka sace mata mota a Kano

dakikun karantawa

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta bayyana kama wasu matasa da ake zarginsu da yanka wata mata a gidanta na aure, suka kuma yi awon gaba da wata a cikin gidan da ke unguwar Sabuwar Gandu a  jihar Kano.

Ana zargin matasan da haura wa gidan matar, suka yanka ta suka kuma cilla ta cika bandakinta a cikin gidan suka kuma sace mota kirar Vibe da ke cikin gidan.

Rundunar ta hannun kakakinta, Abdullahi Haruna Kiyawa ta ce rundunar ta samu korafin ranar 14 ga watan Nuwambar 2020, in da ya ce hukumar bata yi kasa a gwiwa ba wajen kamo matasan da ake zargi, ta kuma samu nasarar kama su a jihar Kaduna.

DABO FM ta tattara cewar matasan da aka kama su hudu ne matasa da shekarunsu basu wuce 20 zuwa 25 ba.

Daya daga cikin matasan mai suna Al’amin Muhammad Bello dan shekara 20 mazaunin jihar Kaduna ya tabbatar da aikata laifin da ake zarginsu da shi.

“Mun shiga Yusra ni da abokai na, wadannan biyu suka tsaya mana a bakin kofa, ni da Yusuf muka shiga cikin gidan. Bayan mun shiga gidan sai na  dauki mukullin mota, muna kokarin fita sai Yusran ta cakumo Yusuf, sai ya buga mata wuka, muka dauke ta muka kai bandaki.”

Sai dai rundunar ta ce an yi nasarar ceto rayuwar matar, bayan an kai ta asibitin Murtala Muhammad kafin daga bisani a mayar da ita Asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano.

A nata bangaren, wadda al’amarin ya rutsa da ita, Yusra Zakariyya mai shekara 20, ta ce tana iya tuna lokacin da wasu suka shigo mata gida suka yo kanta.

“Wasu ne sun shigo, sun yo kai na da wuka, tin daga nan ban kara sanin komai ba.”

Rundunar ta ce da zarar ta kammala bincike, za ta aike da matasa zuwa gaban kotu domin karbar hukunci,

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog